'Zan sa kafar wando guda da Boko Haram'

Jonathan ya sauka daga mulki, ya mika wa Buhari

Asalin hoton, Reuters

Bayanan hoto, Jonathan ya sauka daga mulki, ya mika wa Buhari

Sabon shugaban Nigeria, Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa zai dauki kwakkwaran mataki wajen yaki da Boko Haram.

Ya yi wannan alwashin ne, bayan ya sha rantsuwar kama aiki, inda ya bayyana 'yan kungiyar Boko Haram din da cewar marasa imani ne.

Muhammadu Buhari ya ce zai yi bakin kokarinsa wajen ceto 'yan matan sakandaren Chibok da mayakan kungiyar suka sace sama da shekara guda.

Kazalika shugaban kasar ya ce tattalin arzikin Nigeria ya fada cikin wani mummunan hali.

Muhammadu Buhari dai ya kasance dan takara na farko daga jam'iyyar adawa da ya samu nasarar kada jam'iyya mai mulki wajen zama shugaban kasa a tarihin Nigeria.

Shugabannin kasashe da dama ne da kuma sakataren harkokin wajen Amurka, John Kerry suka halarci bikin rantsarwar a Abuja.